9 Maris 2020 - 10:50
Firai Ministan Riko Na Iraqi Ya Ce Amurka Tana Matsawa Kasar Lamba Na Ta Katse Hulda Da Iran

Firai ministan riko na kasar Iraqi Adel Abdul-Mahdi ya fadawa shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran kan cewa gwamnatin Amurka tana batsawa kasar lamba na ta yanke hulda da kasar Iran.

(ABNA24.com) Abdul-Mahdi ya bayyana haka ne a jiya Lahadi a lokacinda yake ganawa da Ali Shamkhani a birnin Bagdaza, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ta rikita al’amura a yankin Asia ta kudu bayan ficewarta daga yarjejeniyar Nukliyar kasar Iran a ta shekara ta 2015.

Har’ila yau Abdul-Mahdi ya kara da cewa idan ba taimakon kasar Iran wajen yakar kungiyar Daesh wacce ta mamaye kasar Iraqi a shekarummu baya ba, da har yanzun kungiyar tana mamaye da kasar Iraqi. Y ace Iraniyawa sun zubar da jininsu da kare kasar Iraqi daga mamayar kungiyar yan ta’adda.

Daga karshen firai ministan riko na kasar ta Iraqi ya kara da cewa duk tare da matsin lambara kasar Amurka kasar Iraqi ba za ta ci gaba da hulda da makobtanta don amfanan bangarorin biyu.

A nashi bangaren Ali Shamkhani ya ce kasashen Amurka da HKI su ne makiyan kasashen Iran da Iraqi kuma dole ne kasashen biyu su hada kai don fuskantarsu.




/129